6 Faburairu 2021 - 15:10
Iran Ta Yi Maraba Da Kafa Sabuwar Gwamnatin A Kasar Libya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Sa’id Khatibzadeh ya bayyana jin dadin Iran din akan yadda bangarorin siyasar Libya da su ka yi taro a birnin Geneva su ka cimma matsaya akan kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya.

ABNA24 : Kakakin na ma’aikatar harkokin wajen Iran din ya kuma yi fatan ganin cewa gwamnatin rikon kwaryar ta share fagen yadda za a kai ga yin zabe a cikin wannan kasa.

A jiya Juma’a ne dai bangarorin siyasar kasar ta Libya da su ka taru a birnin Geneva, su ka kada kuri’ar zaben sabon shugaban hukumar rikon kwarya Muhammad al-Manfy, da kuma shugaban majalisar shugabancin sannan kuma Pira minista, Abdulhamid al-Dabibah.

Kasar Libya dai ta dade tana fada da rikice-rikicen siyasa, inda aka sami kafuwar gwamnatoci biyu a bagashi da yammacin kasar.

342/